1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INGANTA ZAMAN CUDE-NI IN CUDE-KA A JAMUS.

Yahaya AhmedJanuary 8, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmh

Mehmet Keksin, wani baturke ne da ya zo nan Jamus tun 1980, don yin karatu mai zurfi a jami'a. Yayin da ya iso nan kasar, bai iya ko kalma daya ta Jamusanci ba. Amma kamar yadda ya bayyanar, duk wanda yake da kyakyawar niyya, zai iya kuma cim ma gurinsa. Da wannan jigon ne Mehmet ya fara karatunsa a fannin ilimin halitta a jami'ar Hamburg. A lokaci daya kuma, ya yi aiki da hukumar kula da `yan gudun hijira ta birnin na Hamburg. Daga baya ne kuma, ya rike mukamin mai bai wa matasa baki shawara a kungiyar ciniki da masana'antu ta birnin. Amma a nasa ganin, hakan bai wadatas ba. Dalilin da ya sa ke nan ya kafa wani kamfani wanda ya yi wa suna ATU. Ya dai bayyana cewa:-

"Ma'anar ATU ita ce, kungiyar bai wa masu sana'o'i baki shawara kan yadda za su iya kasancewa masu zaman kansu. A lokacin da muke ba da shawarar, mu kan kuma jawo hankullan bakin kan inganta Jamusancinsu da kuma kara ilimi a nan jamus."

Akwai dai kamfanoni da yawa na baki a nan Jamus. Amma kadan daga cikinsu ne ke bai wa matasa baki horo. Mehmet Keksin kuwa, ya ga horon ma shi ya fi muhimmanci, idan dai ana son a sami nasara a harkar sana'o'i da kasuwanci a nan kasar. Kawo yanzu dai, kamfanin Mehmet ya tura matasa fiye da 500 zuwa kafofin ba da horon sana'o'i daban-daban. Murat Candan, wani baturke mai shekaru 21 da haihuwa, na cikin wadanda suka ci moriyar wannan shirin:-

"Na sami adreshin wannan kamfanin ne daga ofishin kwadago. Da na zo gunsu kuma, sun taimaka mini kwarai, wajen samun gun horo." A halin yanzu dai, Candan ya gama horonsa a fannin ciniki na ketare. A lokacin da yake koyar sana'ar kuwa, ya ce ba don taimakon kamfanin ATU din ba da bai iya ya kammala karatunsa ba.

A galibi, kamfanonin ketare da ke nan Jamus, ba su cika horad da matasa ba, saboda masu kamfanonin da kansu, ba su nakalci harshen Jamusancin sosai ba. Mahmet Keksin dai na ganin wannan babban kuskure ne. Ya bayyana cewa, kamata ya yi duk wanda ya tsai da shawarar zama a nan Jamus, ya kuma yi kokarin koyar harshen. Ta hakan ne zai iya samun saukin tafiyad da harkokinsa.

Akwai baki da yawa a nan Jamus, wadanda ba sa cudanya da sauran jama'a, sai dai a rukunin `yan kasar da suka fito. Turkawa ne dai suka fi yawa a wannan nau'in bakin. sabili da hakan ne kuwa, Mehmet Keskin, ke bai wa duk `yan kasarsa na asali shawara, da kada su kebe kansu daga bainar jama'a. kokari ya kamata su yi, su saba da yanayin da suke ciki, ta hanyar cudanya da sauran jama'a. Wannan dai shi ne muhimmin sakon da yake bayyana wa duk matasan da suka zo neman shawara a kamfaninsa na ATU da ke birnin Hamburg.