1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: An kammala zaben majalisar dokoki

Ramatu Garba Baba
May 12, 2018

A yayin da ake ci gaba da kidayan kuri'u a zaben majalisar dokoki da ya gudana a wannan Asabar, mutane akalla uku aka tabbatar da mutuwarsu a sanadiyar tashin wani bam a yankin Kirkuk.

https://p.dw.com/p/2xbno
Irak Wahl | Sicherheit Wahllokal in Bagdad
Hoto: Reuters/W. al-Okili

An gano biyu daga cikin mamatan wadanda suka fito yin zabe ne yayin da guda ya kasance daya daga cikin masu sa ido kan zaben. Kungiyar IS da ta yi alkwarin kai hari a yayin wannan zaben, ta dauki alhakin kai harin amman kawo yanzu babu tabbacin hakan daga hukumomin kasar.

Wannan zabe shi ne irinsa na farko tun bayan da kasar ta ayyana samun nasara kan 'yan kungiyar da ke da'awar jihadi kuma ana kallon zaben a matsayin wani zakaran gwajin dafi na farin jinin firaministan kasar Haider a-Abadi. Masu aiko da rahotanni sun ce kimanin 'yan takara dubu bakwai daga jam'iyyu daban-daban na kaasar ne ke zawarci kujerun majalisar dokokin kasar guda dari uku da ashirin da tara.