1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: Harin bam ya halaka fiye da mutum 70

Ramatu Garba Baba
September 14, 2017

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a gidan cin abinci a birnin Nasiriya da ke a kudancin kasar Iraki ya halaka mutane 74 tare da raunata wasu da dama.

https://p.dw.com/p/2jytY
Irak Doppelanschlag in der Nähe von Nassirijah
Hoto: Reuters/E. Al-Sudani

Rahotanni daga kasar na cewa da farko wani dan kunar bakin wake ne ya soma tayar da bam din da ke a jikinsa a cikin gidan cin abincin yayin da wasu maharan da ke a wajen ginin suka bude wuta akan jama'ar da ke harabar gidan cin abinci, a wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta tabbatar da alkaluman mamatan ta kuma ce akwai wasu Iraniya hudu a cikin mamatan.

Ana dai fargabar alkaluman mamatan ka iya haurawa ganin munin lamarin, harin na zuwa a yayin da dakarun gwamnatin kasar ke cewa suna kokarin fatatakar mayakan kungiyar IS da ayyukan su ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane a kasar, Kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai tagwayen hare haren na wannan rana.