1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ka iya fadawa cikin wani yakin basasa

August 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bunv

Shugaban rundunar sojin Amirka a Iraqi, janar John Abizaid ya ce Iraqi ka iya fadawa cikin yakin basasa. Janar din ya nunar da haka ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawan Amirka dake kula da aikin soji a birnin Washington. Abizaid ya ce tashe tashen hankula a Bagadaza sun yi muni fiye da yadda ake zato.

Da farko jakadan Birtaniya a Iraqi mai barin aiki, William Patey ya nuna irin wannan fargaba, inda yace da akwai yiwuwar barkewar wani yakin basasa a Iraqin, wanda zai tarwatsa kasar. A cikin wasikarsa ta karshe da ya aikewa gwamnatin Birtaniya, jakadan ya ce yanzu an fi fuskantar barazanar fadawa wani yakin basasa gadan-gadan maimakon samun nasarar girke wata gwamnatin demukiradiyya a Iraqi. A ci-gaba da tashe tashen hankula a Bagadaza, a yau an kashe akalla mutane 10 sannan 14 sun jikata a wani harin bam da aka kai a gefen hanya a unguwar Al-Amin dake kudancin babban birnin na Iraqi.