1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta Kai farmaki kan 'yan kungiyar IS

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 24, 2016

Sojojin Iraki sun kwato garin Sinjar daga hannun kungiyar IS bayan da suka kai wani farmaki bisa tallafin sojojin kawance na kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1IJPX
Militärische Ausbildung für Kurden in Deutschland
Hoto: picture-alliance/AP Images/M. Sohn

Dakarun gwamnatin Iraki sun kaddamar da samame kan mayakan kungiyar IS a birnin Mosul da kewaye, da nufin karya lagon masu kaifin kishin addini a yankin arewacin kasar. Tuni ma rahotanni suka nunar da cewar hakar sojojin na Iraki ta fara cimma ruwa, inda suka yi nasarar fatattakar 'yan IS a garin Sinjar da ke kan iyakar Iraki da Siriya.

Ita dai gwamnatin Iraki ta hada gwiwa da dakarun kasashen yammacin duniya, wajen murkushe tsagerun da suka mamaye wasu manyan birane na arewacin kasar ciki har da Mosul. Shekaru biyun da suka gabata ne dai mayakan na IS suka kwace ikon birnin Mosul daga hannun gwamnati.

Tuni ma wani dan kasar ta Iraki ya bayyana farin cikinsa, inda ya ce "Ina fata cewar somin tabi ne a yunkurin da gwamnati ke yi na raba Iraki kwata-kwata da 'yan ta'adda."