1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta karyata rahotan MDD

January 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuU8

Hukumomin kasar Iraki sun karyata rahotan MDd dsake nuni dacewa akalla mutane dubu 34,da dari 4 ne suka rasa rayukansu a shekarar data gabata kadai.Kakakin Premiern Irakin Nuri al-Maliki,Ali al-Dabbagh ya bayyana cewa rahotan da mdd ta gabatar a ranar talata adanagane da adadin wadanda suka rasa rayuknasu a Irakin,bai yi daidai da ainihin adadin wadanda suka mutun ba.Mdd ta rubuta wannan rahoto nata ne bisa ga kiyasin maaikatar kula da lafiya ta Iraki,da adadin data samu daga asibitocin kasar ,da kuma wadanda ta samu daga wuraren ajiye gawawwaki.