1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Ayatollah ya soki hukumomin Saudiyya

Salissou Boukari
May 28, 2017

A wani jawabi da ya yi a farko-farkon soma azumin watan Ramadana, jagoran Muslunci na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya soki lamirin gwamnatin Saudiyya da kuma ta kasar Amirka.

https://p.dw.com/p/2dhyL
Iran Palästinakonferenz in Teheran Ajatollah Ali Chamenei
Hoto: Mehrnews

Jagoran na Muslunci na kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce " babban abun takaicin shi ne, na wasu mutane da ba su da cancanta ba, amma sun dauki makomar al'ummar Muslumai a hannunsu, kaman wasu gwamnatoci irin na Saudiyya. Ya ce a bayyane suna nunawa yin biyeyya ga Alkur'ani mai tsarki, amma kuma a aikace suna yin abubuwan da suka saba wa koyarwa ta Alkur'ani. Ya ce suna nuna amintaka tare da bayar da arzikinsu ga abokan gaba, maimakon su yi amfani da arzikin domin walwalar jama'arsu.

Ayathollah Ali Kkamenei ya kara da cewa, tunda Amirkawa sun fada, sai kawai su yi ta kwasar arzikinsu suna ba su tamkar ana tatsar saniya, sannan daga bisani su zo su hallakasu. Yayin wani babban zaman taro ne dai na ran 21 ga watan nan na Mayu a birnin Ryad, Shugaban Amirka Donald Trump ya soki kasar ta Iran tare da yin kira ga kasashen Musulmi da su mayar da ita saniyar ware.