1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da cikan waadin majalisar dunkin duniya

Zainab A MohammadAugust 31, 2006
https://p.dw.com/p/BtyQ
Shugaba Ahmadinejad na Iran
Shugaba Ahmadinejad na IranHoto: AP

Iran naciga da bunkasa sinadran Uranium,duk da cikan waadin da mdd ta debar mata,na dakatar da shirin ko kuma ta fuskanci takunkumin komitin sulhu.

Shugaban hukumar kula da Nuclear ta mdd,ya bukaci kasashe dasu sake gyaran yarjejeniyar haramta yaduwar makaman nuclear,saboda muhimmancinsa wajen tsaro a duniya ,kana zai tabbatar dacewa sabbin kasashe dake da wakilci basu kera makaman nuclear ba.

Yarjejeniyar wadda ta haramta harba makaman nuclear,bazata iya tasiri ba har sai wakilan kasashe guda 44 da suka halarci taron kwance makamai na shekarata 1996,sun sake yi mata gyara .

Kasashe 34 dake cikin wannan yarjejeniyar ne kadai suka yi mata kwaskwarima .kasashe da suka ki ayi gyaran kuwa sun hadar da Amurka da Sin da India da Pakistan da Izrela da koriya ta arewa

Babban Directan hukumar kula da yaduwar Nuckear a doron kasa ta mdd,Mohamme3d Elberadei,yace hakan ne kadai zai iya dakatar da kasashe daga cigaba da kera makaman Nuclear.

Adaidai lokacin da waadin naIran ke cika,shugaba Mahmoud Ahmadinejad yayi jawabin dake dada jaddada manufar kasarsa na cigaba da sarrafa sinaran Uranium duk da matsin lamba datake fuskanta daga kasashen yammaci.

Shugaban Iran din yace kasaresa nada yancin samarwa alummarta ingantaccen wutan lantarki don haka babu gudu babu jada baya.

Sakatare General na mdd Kofi Annan yace wannan waadi ya cika,sai dai komitin sulhun bazata gaggauta daukan mataki akan Iran ba,sai bayan kasashe shida dake tattauna matsalar sun gana a mako mai zuwa.

Tun a baya dai kasashe biyar dake da zaunanniyar kujera a komitin sulhun hade da Jamus sun alkawartawa Iran sakayya mai tsoka idan har ta dakatar da sarrafa sinadran Uranium.

Shugabar gwamnatin Angela Merkel,har yanzu kofa bude wa kasar Iran a dangane da wannan tayin sakayya,duk da cikan wannan waadin.Sai dai tace Tehran zatayi dana sani idan har tabar wannan dama ya wuce.

Shi kuwa ministan harkokin wajen faransa Philippe Douste-Blazy.cewa yayi har yanzu bai fidda tsammanin cewa Iran zata amince da bukatun kasashen duniya ba,na watsar da harkokin bunkasa uranium dinta.

Tun adaren jiya nedai shugaba Ahmadinejad ya yi kira ga kasashen turai da suyi watsi miyagun manufofin Amurka,wadda ta yanke huldar diplomasiyya da Iran din a 1979,tare dacewa kofarsa bude take garesu domin tattauna shirin Nuclearnta.

Rahotanni daga headquatar komitin sulhun mdd dake Brussels din kasar Belgium na nuni dacewa ,jamiin kulawa da harkokin ketare na kungiyar Javier Solana zasu gana da babban jamiin Iran kann harkokin Nuclear Ali Larjani ,bayan sun tattauna ta wayan tangaraho.

Ayayinda a gobe ne kuma Mr Solana zai gana da ministocin harkokin wajen kungiyar ta Eu a Finland,inda akesaran zaiji martanin kasashen turan adangane da wannan kunnen uwar shegu da Iran tayi,adangane da dakatar da bunkasa uranium dinta,batu dake barazana wa kokarin diplomasiyya da aka debi watanni anayi.