1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da hukumar IAEA sun amince da gudanar da bincike a tashar nukiliyar Arak

July 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuFe

Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA sun amince da wasu sabbin matakai dangane da sa ido kan shirin nukiliyar Iran. Hakan kuwa ya hada har da gudanar da bincike a mako mai zuwa a tashar nukiliya ta Arak wadda ake takaddama akan ta. Sannan mako guda bayan haka za´a cimma matsaya akan sauran batutuwa da suka hada da asalin sinadarin plutonium wanda masana ilimin kimiyar Iran suka yi nazari a kai. An cimma wannan daidaito ne tsakanin daraktan sashen fasaha na hukumar IAEA Olli Heinonen da mukaddashin majalisar tsaron kasar Iran Jawad Waidi a birnin Vienna. To sai dai jami´an diplomasiyar yamma sun yi kashedi game da sanyan dogon buri na warware takaddamar nukiliyar Iran din cikin gaggawa.