1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da kasashen yamma a game da kokarin mallakar makamin Atom

Ibrahim SaniApril 13, 2006

Ko shin kwalliya zata biya kudin sabulu a game da ziyarar El Baradei a Iran..

https://p.dw.com/p/Bu0e
Hoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Ya zuwa yanzu dai tuni El Baradei ya fara tattaunawa da wasu manya manyan jami´an gwamnatin ta Iran,don janyo hankalin ta data dakatar da aniyar ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium.

Wannan ziyara dai ta El Baradei a cewar rahotanni tazo ne kwanaki kadan bayan shugaba Mahmud Ahmadinajad na Iran ya tabbatar da cewa, kasar ta Iran ta samu galabar inganta sanadarin na Uranium a mataki na farko, wanda a nan gaba hakan ka iya bata damar kera makamin Atom.

Kasar ta Iran ta ci gaba da aiwatar da wannan aniya tata ne, duk kuwa da wa´adi na ranar 28 ga watan nan da kwamitin sulhu na Mdd, ya bata nata dakatar da wannan aniya, ko kuma ta fuskanci fushinta.

Kafin dai shugaban hukumar ta IAEA Mohd El Baradei ya fara wannan tattaunawa da wasu daga cikin jami´an gwamnatin na Iran, kafafen yada labaru sun rawaito shi yana fadin cewa............

Zamu tattauna hanyoyin da kasar ta Iran zata martaba dokokin kasa da kasa,musanmamma na dakatar da ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium da kuma daina daukar duk wasu matakai dake da nasaba da haka, har zuwa lokacin da zamu warware dukkannin takaddamar dake tattare da wannan aniya data sa a gaba.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labaru sun rawaito wasu daga cikin jami´an hukumar ta IAEA na fadin cewa da wuya wannan ziyara ta El baradei ta haifar da da mai ido, bisa furucin da Ahmadinajad yayi na cewa babu gudu babu ja da baya a game da wannan aniya da kasar tasa a gaba.

A dai lokacin da shugaba Ahmadinajad ya gabatar da jawabin sa ya tabbatar da cewa, a yanzu haka kasar ta Iran ta shiga sahun kasashen duniya dake da fasahar kera makamin na Atom.

Bisa kuwa wannan bayani na Ahmadinajad, daya dauki hankalin kasashen yamma, tuni mahukuntan Amurka suka bukaci Mdd data dauki kwararan matakai na ladaftar da kasar, to amma kasar Russia cewa tayi akwai bukatar duba al´amarin cikin ruwan sanyi don kada aikin garaje ya haifar da da na sani.

Ita ma dai kasar Sin cewa tayi akwai bukatar a tunkari wannan matsala ta hanyar diplomasiyya, a mai makon yin amfani da karfin soji. Bisa hakan tace a gobe juma´a zata aike da manzon ta izuwa kasashen na Iran da Russia don tattaunawa wannan batu bisa manufar nemo bakin zaren warware ta.

A kuwa yayin da ake ci gaba da wannan takaddama, babban sakataren Mdd wato Mr Kofi Anan cewa yayi...........

Tun da kasar ta Iran ta dage cewa nukiliyarta ta zaman lafiya ce, bata tashin hankali ba, to kamata yayi ta tabbatarwa da gamayyar kasa da kasa hakan ta hada hannu da hannaye guri guda dasu na samo bakin zaren warware rashin fahimtar dake akwai.

Ya zuwa yanzu dai ba sau daya ba sau biyu ba, mahukuntan na Iran ke tabbatar da cewa, nukiliyar da suke kokarin kerawa ta inganta rayuwar yan kasar ce, amma bata haifar da tsugune tashi ba.