1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da kasashen yammaci

Zainab A MohammadMarch 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7W

Iran

Iran ta lashi takobin cewa kasashen yammaci basu isa su barazana harkokinta na Nuclear ba,ayayinda shugaba Mahmoud Ahmadinejad yace babu wanda zai tozartawa Tehran.

Wadannan kalamai dai sunzo ne a daidai lokacin da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tace Iran ce zata zame babbar kalubale wa tsare tsaren Amurka a yankin gabas ta tsakiya.Rasha wadda ke fatan bazaa gurfanar da Iran din gaban komitin sulhun mdd domin kakamata takunkumi ba,ta bukaci Tehran data bada cikakken hadin kai wa masu bincike na m,dd.

Dayake jawabi yini guda, da bayyanan alamun cewa komitin zata dauki matakan ladabtar da Iran,shugaban addinin islama na Iran Ayatollah Ali Khamenei,yayi kira ga jamiaan komitin da kada su amince da matsinlambar da kasashen turai keyi.Yace koda iRan ta dakatar da harkokin makamashinta na nuclear ayau din nan,labarin bazai tsaya nan ba ,domin Amurkawa zasu bullo ta wata hanya da wani zargin.Sai dai kuma jagoran addinin Islaman yayi kira dangane amfani da adalci wajen tantance gaskiyar lamarin,batu kuma da zai iya kwantar da suka da ake samu daga cikin kasar ta Iran.A jawabin dayayi ta kafofin yada labaru ayau,shugaban Iran Ahmadinejad,yace babu kasar data isa tayiwa kasarsa barazana ta kowace hanya.