1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na ƙoƙarin yin tasiri a Afirka

December 18, 2009

Bisa ga dukkan alamu Iran na neman fakewa ne da guzuma domin ta harbi karsana a dangantakarta da ƙasashen Afirka

https://p.dw.com/p/L85U
Shugaba Mahmoud Ahmadinejad da shugaba Hugo ChavezHoto: AP

Ɗaya daga cikin batutuwan da jaridun na Jamus suka mayar da hankali kansa a wannan makon dai shi ne yadda ƙasar Iran ke neman yin tasiri a ƙasashen Afirka. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi nazari tana mai cewar:

"Daga cikin manufofin ƙasar Iran har da ƙoƙarin faɗaɗa dangantakarta da ƙasashen Afirka da na kudancin Amirka. A ƙarƙashin wani mataki na haɗin kai don adawa da sabon salo na mulkin mallaka, ƙasar ta Iran ke ƙoƙarin neman kasuwa ga man fetir ɗinta da kuma motocin da take ƙerawa. Wannan shi ne ainihin dalilin ziyarar da shugaba Ahmadinajad ya kai baya-bayan nan ga wasu ƙasashen yammacin Afirka guda biyu da kuma wasu ƙasashe uku na Latinamirka."

A cikin wani rahoton da ta bayar baya-bayan nan akan lardin Darfur na ƙasar Sudan Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi wata ƙungiyar taimakon 'yan gudun hijira ta Jamus da laifin tallafa wa 'yan tawaye a lardin nna Darfur. Jaridar Frankfurter Rundschau ce ta faɗi hakan, ta kuma ƙara da cewa:

Entführung Ärzte ohne Grenzen Mitarbeiter in Darfur
'Yan makaranta a DarfurHoto: AP

"Ana zargin ƙungiyar ta Jamus ne da laifin tara wasu kuɗaɗe da sunan taimaka wa wasu makarantu guda uku a Tine, waɗanda a haƙiƙanin gaskiya, babu su kwata-kwata, kuma duk wanda ya karanta rahoton zai yi zaton cewar kuɗaɗen sun kwarara ne zuwa baitul malin ƙungiyar tawaye ta JEM, wadda kawo yanzu take adawa da shiga shawarwarin sulhu da fadar mulki ta Khartoum. To sai dai kuma bisa ga dukkan alamu wannan zargin ba ya da toshe, saboda ƙungiyar, wadda ta haɗa manyan masana dake gudanar da ayyukansu na bincike a Darfur ta gabatar da cikakkun bayanai game da makarantun abin da ya haɗa har da hotunansu da kuma yawan kuɗin da ake batu kansu da yadda aka aiwatar dasu. Kazalika da ayyukan da ake shirin gudanarwa daga abin da ya rage daga jumullar kuɗin na Euro dubu saba'in da ɗaya."

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta Human Rights Watch ta zargi sojan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a game da hannu a kashe-kashe na gillar da ake zargin sojoji da 'yan tawayen Hutu da aikatawa a gabacin ƙasar Kongo. A lokacin da take bayani jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Flüchtlinge im Kongo
Farar hula ne suke fama da raɗaɗin yaƙi a KongoHoto: dpa

"Farar hula su ne suka fi fama da raɗaɗin yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawayen Hutu a a gabacin ƙasar Kongo. A wani binciken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar ta gano cewar akwai haɗin kai tsakanin sojojin na Kongo da 'yan tawayen FDLR, waɗanda a hukumance suke iƙirarin yaƙar juna, kuma dukkan sassan biyu na tursasa wa farar hula in ji ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta Human Rights Watch. To sai dai kuma ƙungiyar ta ce tare da taimakon kayan aiki daga askarawan kiyaye zaman lafiya na Monuc ne sojojin Kongo ke da ikon tafiyar da yaƙin. Kuma ko da yake ƙungiyar bata yi zargin maƙarƙashiya ba, amma ta ce wajibi ne a sake bitar ayyukan rundunar ta Monuc."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala