1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Iran na bin sharuddan da aka gindaya mata

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 27, 2016

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta bayyana cewa kasar Iran na aiki da dukkan sharuddan da aka gindaya mata kan makamashin nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/1IvR9
Darakta janar na hukumar IAEA Yukiya Amano
Darakta janar na hukumar IAEA Yukiya AmanoHoto: Reuters/L. Foeger

Wadannan sharudda dai an gindaya wa Iran su ne yayin cimma yarjejeniyar da suka yi da kasashe shida da ke fada a ji a duniya kan makamashin nukiliyar Iran din. A wani rahoto da hukumar ta IAEA ta fitar, ta nunar da cewa Iran na cika dukkan alkawuran da ta dauka yayin cimma wannan yarjejeniya a bara, kana tana barin wakilan hukumar su kai ziyarar gani da ido a tashoshin nukiliyarta. Wannan rahoto dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amirka da Japan suka yi kira da a kawo karshen yaduwar makaman nukiliya a duniya, yayin wata ziyara da shugaban Amirkan Barack Obama ya kai yankin Hiroshima na Japan din da harin makaman nukiliyar Amirka ya dai-daita a shekara ta 1945. Iran dai ta cimma yarjejeniyar rage sarrafa makamashin nukiliyarta da kasashe shida masu fada a ji a duniya, ta yadda su kuma a hannu guda za su cire mata takunkuman karya tattalin arzikin da suka kakaba mata na tsahon shekaru.