1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na kokarin ganin an samu zaman lafiya a Iraq

November 28, 2006
https://p.dw.com/p/BuZy

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad yace kasar sa a shirye take tayi duk abinda ya dace ,don ganin zaman lafiya ya tabbata a Iraq.

Mr Ahmadinajad ya fadi hakan ne, jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasar ta Iraqi Jalal Talabani, wanda ya fara ziyarar aiki a kasar jiya.

Rahotanni dai sun rawaito cewa ziyarar ta Talabani ta samu dan tsaiko ne, bayan da mahukuntan Iraqi suka sa dokar ta baci a birnin Bagadaza jiya, bayan tashin wani bom daya halaka mutane sama da 200.

Faruwar wannan al´amari dai ya haifar sakataren Mdd mai barin gado, wato Mr Kofi Anan cewa, matukar ba´ayi hankali ba to yakin basasa ka iya barkewa a kasar ta Iraqi.

Tuni dai fadar white House ta karyata wannan zargi da cewa bashi da tushe balle makama.

Ana dai sa ran cewa a wani lokaci ne a wannan makon, shugaba Bush zai sadu da faraministan na Iraqi, Nuri Al Maliki a Jordan, don tattauna halin da ake ciki a iraqin.