1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na samun ci gaba a sarrafa sanadarin Uranium

April 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2I

Shugaba Mahmud Ahmadinajad na Iran, ya tabbatar da cewa an samu ci gaba dangane da sarrafa sanadarin Uranium da kasar sa keyi.

Bisa hakan, shugaban ya tabbatar da cewa a yanzu haka Iran na daga cikin sahun kasashen duniya dake da fasahar kera makamin nukiliya.

Shugaban daya fadi hakan a dazu dazun nan , a wani taron manema labarai daya gudanar, ya kara da cewa kasar zata ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium har zuwa lokacin da zata cimma burin data sa a gaba.

Shugaba Ahmadinajad, wanda yake ci gaba da fuskantar suka daga kasashen yamma a game da wannan aniya, ya kara nanata cewa nukiliyar da suke kokarin kerawa ta inganta rayuwar yabn kasar ce , amma bata tashin hankali ba.