1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IRAN SHEKARU 25 DA JUYIN JUYA HALIN ISLAMA.

Yahaya Ahmed.February 10, 2004

-Take: "Allah.......,Iran" -

https://p.dw.com/p/Bvly

Wannan dai shi ne taken da kafofin yada labaran
kasar Iran ke ta sakawa yanzu a gabannin duk
shirye-shiryen da za su gabatar. Wato da farko
dai Allah, shi ne mafi a'ala. Sa'annan kasar ta
Iran ta biyo baya. Kafin juyin juya halin dai,
babu ma wanda ya isa ya saka irin wannan taken
a shirye-shiyen kafofin yada labarai. A wannan
lokacin, daliban kasar sun yi ta zanga-zanga ne
don nuna adawa ga mulkin almubazzaranci da
danniyar da sarkin sarakuna Shah Reza Pahlavi
ke yi wa `yan kasarsa. Ban da dai daliban,
shugabannin addinin kasar ma sun yi ta tasu
zanga-zangar, ta nuna bacin ransu ga abin da
suke gani kamar tabarbarewar tarbiyya da ake ta
kara samu, sakamakon angizon da kasashen Yamma
ke da shi a kasar, musamman ma dai Ingila,
sa'annan daga baya kuma Amirka.
Su dai shugabannin addinin, sun kokarta kwarai
wajen fadakad da jama'a a masallatai don su
goyi bayan juyin juya halin da suke shiryawa.
Ba abin mamaki ba ne kuwa, ganin yadda dubu
dubatan jama'a suka fito kan titunan birnin
Teheran suka yi wa shugaban darikar shi'itin
kasar, Ayatullah Ruhullah Khomeini marhaba, a
loakcin da ya dawo daga zaman gudun hijiran da
ya yi a Faransa:-

Kafin dawowar Aayatullahin ma, an rarraba
dimbin yawan kaset da ya wallafa ga jama'ar
kasar, inda yake bayyana irin illolin da
angizon kasashen Yamma zai janyo wa kasar.
Hakan dai ya sa shugabanin addinin sun sami
farin jini a bainar jama'a. Ta hakan ne kuma,
aka cim ma nasarar yin juyin juya halin. Amma
bayan an hambare sarkin sarakuna Shah Reza
Pahlavi, sai kuma aka shiga wata gwagwarmaya
tsakanin shugabannin addinin da masu bin wata
akida, wadanda ba su amince da kafa jumhuriyar
islaman ba. Abin da ya fi damun Imam Khomeini a
wannan lokacin dai, shi ne samun hadin kan duk
`yan kasar. Sabili da haka ne kuwa, a farkon
jawabinsa ga al'umman kasar ya ce:-
"Muna yi wa duk bangarorin al'umman kasar nan
matukar godiya. Saboda wannan nasarar da muka
samu ta yiwu ne sakamakon hadin kan duk rukunan
kasar nan. Hadin kai tsakanin musulmi da `yan
tsirarun wasu addinai, hadin kai tsakanin
jami'o'i da fannonin ilimin addini na kasar
nan, sa'annan hadin kai tsakkanin malaman
addini da `yan siyasa. Bai kamata mu taba
mantawa da kwazon da wannan hadin kan ya samar
wa al'umman kasar nan ba. Kuma wajibi ne mu san
cewa wannan hadin kan, shi ne dalilin samun
nasararmu. Ya kamata kuwa, mu yi duk iyakacin
kokarinmu wajen kare shi."
Ba a dai sami cikakken kwanciyar hankali a Iran
din bayan juyin juya halin ba. Ba a dade da
hambarad da Shah ba ne kasar Iraqi, karkashin
mulkin Saddam Hussein, ta kai wa Iran hari,
abin da ya janyo wani mummunan yaki, wanda
kasashen biyu suka shafe shekaru 8 suna ta
gwabzawa tsakaninsu. Bugu da kari kuma, sai
Amirka, wadda mamaye ofishin jakadancinta a
birnin Teheran da daliban kasar suka yi ya kada
mata hanci, ta sanya wa Iran takunkumi. Kai
tsaye dai sai kassar ta sami kanta cikin wani
rudami. Shugabannin addinai da suka sami
mukamai na siyasa, ba su san yadda za su
tafiyad harkokinsu ba. A hankali dai, sai aka
sami wani rukuni na masu mulki, wadanda kuma
ba addinin ne ya dame su ba, sai azurta kansu
da iyalansu. Hakan dai ya bata wa talakawan
kasar ransu, abin da ya sa kuma ke nan jama'a
da yawa ke nuna adawarsu ga shugabannin addinin
kasar a ahalin yanzu.
Daliban kasar dai sun ce, ba za su shiga cikin
wani shirin juyin juya hali ba kuma, amma duk
da haka za su kaurace wa zaben majalisar
dokokin da za a yi a cikin wannan watan. Kamar
yadda wani dalibi da ya bukaci kada a ambaci
sunansa ya bayyanar:-
"Mun dai ga yadda duk bangarorin suke. A zaben
da aka yi a da can, `yan masu bin ra'ayin
mutanen dauri ne suka fi rinjayi a majalisa. A
halin yanzu kuma, masu neman sauyi ne ke da
rinjayin. Amma dukkaninsu, babu wanda ya yi
mana wani abin a zo a gani. Sabili da haka ne
nake ganin cewa, ba wanda zai fita zuwa zabe
kuma."
A halin yanzu dai majalisar shurar kasar, ta
haramta wa `yan takara fiye da dubu 2 tsayawa a
zaben majalisar dokokin da za a yi, a cikinsu
kuwa har da `yan majalisa kusan 80. Daya daga
cikinsu, Behzad Nabavi, ya yi kakkausar suka ga
mahukuntan kasar na yanzu da cewa:-
"Tafarkin siyasar da shugaba Khomeini ya tsara
mana a da dai, ba shi masu bin ra'ayin mazan
jiya suke gabatar wa matasanmu yanzu ba. Da
jama'a sun san cewa haka shugabannin addinin za
su dinga tafiyad da harkokin kasar nan, na
tabbatar, da babu wanda zai goyi bayan juyin
juya halin da aka yi."