1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta baiwa Hugo Chavez lambar girmamawa

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoX

Iran ta karrama shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez da lambar yabo mafi daraja saboda goyon baya da yake nunawa Tehran a taƙaddamar ta ta nukiliya. Shugaban na Venezuela Hugo Chavez ya buƙaci ƙasashen duniya su tashi tsaye a kan Amurka. Chavez ya baiyana shugaban Amurka George W Bush da cewa shaidani ne, ya kuma yi tur da Allah wadai da Israila a bisa abin da ya baiyana da cewa taáddanci da kuma rashin hankali a hare haren da take yi a Lebanon. Hugo Chavez ya yi kira ga alúmar duniya, su haɗa karfi wuri guda domin ganin bayan Amurka. Shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya miƙawa Hugo Chavez tambarin zinare a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a jamiár Tehran tare kuma da yi masa jinjina a dangane da goyon bayan da yake baiwa Iran. A watan fabrairun da ya gabata, ƙasar Venezuela ta ƙi amincewa da shawarar hukumar makamashin nukiliya IAEA na gabatar da Iran ga kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya.