1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta bukaci Palasdinawa su ci gaba da gwagwarmaya

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGa

Shugaban addini na kasar Iran, wato Ayatolla Ali Khamenei ya bukaci alummar Palasdinawa da kada su gajiya wajen ci gaba da gwagwarmayar neman yancin kasar su.

Ayatolla Ali khomeni ya fadi hakan ne a yayin da yake zantawa da daya daga cikin kusoshi na kungiyyar Hamas dake gudun hijira, wanda ya kawo masa ziyara.

Wannan dai kalami na shugaban addinin kasar na a matsayin na baya bayan nan ne dake nuna kyama da tsana ga Israela daga bangaren mahukuntan na Iran.

Idan dai za a iya tunawa, yan kwanaki kadan da suka gabata ne shugaban kasar ta Iran Ahmadinajad ya kira kasar ta israela a matsayin Kari a sahun kasashe na duniya.

Kana a daya hannun ya nuna shakku game da batun kisan kiyashi daya wanzu ga bani Israelan ,da cewa idan akwai kanshin gasskiya game da hakan to kamata yayi a tashi kasar ta Israela daga inda take yanzu izuwa nahiyar Turai.

Game da wadan nan kalamai kuwa, da yawa daga cikin kasashen duniya sun yi Allyah wadai dasu da cewa kalamai ne na tashin zaune tsaye.