1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce ba za ta dakatad da ayyukan sarrafa sinadarin yureniyum ba.

August 20, 2006
https://p.dw.com/p/BumC

Ƙasar Iran ta fito fili ta bayyana cewa, ko kaɗan ba ta da niyyar soke shirye-shiryenta na sarrafa sinadarin yureniyum, wanda zai ba ta damar samar wa kanta makamashin nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Hamid Reza Asefi ne ya bayyana haka yau a birnin Teheran, a wani taron maneman labarai. Jami’in ya ƙara da cewa, soke shirin zai kasance wani koma baya ke nan ga Iran, sabili da haka babu wannan batun ma a ajandar ƙasar.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya dai ya bai wa Iran har zuwa ran 31 ga wannan watan ne, na ta dakatad da ayyukan sarrafa yureniyum ɗin, in ko ba haka ba, za ta sanya mata takunkumi. A ran talata mai zuwa ne Iran ɗin ta ce za ta ba da amsa ga ƙunshin tayin da ƙasashen Yamma suka yi mata na ba ta damar samun wasu fa’idoji idan ta soke shirye-shiryenta na sarrafa makamashin nukiliyan gaba ɗaya. Ƙasar Jumhuriyar Islaman dai ta sha yin watsi da damuwar da ƙasashen Yamma ke nunawa, ta cewa za ta yi amfani da shirin samar da makamashin nukiliyan ne wajen sarrafa makaman ƙare dangi. Har ila yau mahukuntan birnin Teheran na nanata cewa, shirin da suka sanya a agaba, na samar wa ƙasarsu makamashin wutar lantarki ne kawai ta hanyar hannunka mai sanda.