1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce tana da kyakkyawar aniya a shirinta na nukiliya

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKP

Iran ta ce mika wasu takardu dake bayanin yadda ake harhada wani bangare na makamin nukiliya ya nuna kyakkyawar aniyar ta dangane da shirin nukiliyarta da ake takaddama a kai. Takardun wadanda Iran ta ce ta samo su daga wani cinikin bayan fage a shekarar 1987, amma ba ta taba amfani da su ba. Takardun dai sun yi bayanin yadda ake sarrafa sinadarin uranium, inji wani rahoto da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta bayar a jiya juma´a. Mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Mohammad Saidi ya ce rahoton na hukumar IAEA bai ce kasar sa ta karya ka´idojin yarjejeniyar da aka kulla akan wannan batu ba.