1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta jaddada aniyar ta, ta samar da makamashin nuklea

February 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv84

A wata sanarwa da ta hiddo yau talata, gwamnatin kasar Iran, ta jaddada aniyarta, ta ci gaba da ayyukan samar da makashin nuklea, batun da har yanzu, a ke kai ruwa rana a kana sa, tsakanin Iran din, da kasashen masu fada aji a dunia.

Idan ba a manta ta ba, kungiyar gamayya turai, da Amurika, sun samu nasara ciwo kan hukumar yaki da yaduwar makaman nuklea, ta kasa da kasa, da gurfanar da Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.

A satin da ya gabata, kasar Rasha da ke goyan bayan Iran, ta bukaci shiga tsakani, domin warware takkadamar.

Bangarorin 2 su yanke shawara tantananawa daga 16 zuwa 20 ga watan da mu ke ciki.

Shima ministan harakokin wajen China, yayi hanunka mai sanda,ga turai da Amurika, tare da shawarta su, su koma shawarwari a game da matsaklar ta kasar Iran.