1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta nuna shirin yin shawarwari akan shirin ta na nukiliya

May 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuyS
Shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad na Iran ya ce a shirye ya ke ya fara tattaunawa da kasashen duniya game da shirin nukiliyar kasar sa da ake takaddama akai. To amma shugaban ya ce ba zai tattuna da gwamnatocin kasashen dake barazanar kaiwa kasar harin bama-bamai. Shugaban ya furta haka ne a karshen taron kolin kasashe masu tasowa 8 wadanda musulmi suka fi yawa a cikinsu, wanda ya gudana a tsibirin Bali na kasar Indonesia. Ahmedi-Nijad ya tabbatar da cewa Iran zata hada kai da kasashe a fannin fasahar nukiliya a karkashin ka´idojin yarjejeniyar da ta hana yaduwar makaman nukiliya a duniya. A gun taron Indonesia ta ba da sanarwar zata gina tashar makamashin nukiliya kafin shekara ta 2015.