1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta sanarda komawa aikin inganta makamashin atom

January 3, 2006
https://p.dw.com/p/BvDu

A yau kasar Iran ta sanarda komawa bincike game da makamashin nukiliya,mataki da ake ganin zai tunzura Amurka da kuma Kungiyar Taraiyar Turai,wadanda suke tsoron cewa,Iran tana kokarin kera makaman nukiliya ne.

Muhammad Saeedi,shugaban hukumar kula da makamashin atom na Iran,yace gwamnatin Iran ta sanarda hukumar hana yaduwar makaman nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya a rubuce cewa,nan bada jimawa ba zata koma kan bincikenta na inganta makamashin atom a kasar.

Wannan sanarwar kuwa tazo ne a dai dai lokacinda kakakin maaikatar harkokin wajen Iran Hamid reza Asefi,ya baiyana cewa,Iran tana shirin kin amincewa da tayin da kasar Rasha tayi na sarrafa makamashin Iran a cikin kasar ta Rasha,a kokarinta na kawo karshen rikicin nukiliya tsakanin Iran da kasashen yamma.

Nan gaba cikin wannan wata ne zaa koma teburin tattauna batun nukiliya na Iran.