1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta tura wa Katar da abinci mai yawa

Mouhamadou Awal Balarabe
June 11, 2017

Gwamnatin Iran ta kai wa Katar daukin abinci bayan da makwabtanta suka yi fushi da ita kuma suke neman mayar da ita saniyar ware bisa zargin marar hannu a ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2eTZS
Katar Lebensmittel Blockade
Hoto: Getty Images/AFP

Kasar Iran ta aike da jirage biyar na abinci zuwa Katar bayan da kasashen Saudiyya da Bahrain da kuma Hadeddiyar Daular Larabawa suka katse hulda da ita. Kakakin kanfanin jiragen saman Iran Air wato Shahrokh Noushabadi ne ya yi wannan bayani a birnin Teheran, inda ya kara da cewar jirgi na shida wanda shi ma ke dauke da Tonne 90 na abinci na tafe zuwa Doha.

Shi ma shugaban tashar jiragen ruwan Dayyer Mohammad Mehdi Bonchari ya bayyana wa kanfanin dillancin labaran Tasnim cewa an loda Tonne 350 na kayayyakin bukatun yau da kullum a jiragen ruwa uku domin aikewa da su Katar.

Tun ranar Litinin da ta gabata ne Karamar kasar ta katar ta zama 'yan baya ga dangi bayan da kasashen da ke makwabtaka da ita suka zargeta da mara wa ayyukan ta'addanci baya. Lamarin da ya sa kasashen rufe iyakokin da gwamnatin Katar ke amfani da su wajen shigar da abinci a cikin kasar.

Iran da Rasha da kuma Turkiyya sun yi kira ga bangarorin biyu da su zauna kan teburin tattaunawa don warware rikicin da ke tsakaninsu.