1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi barazanar ficewa daga shawarwarin da ake yi kan batun makamashin nukiliyanta.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoP

Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta yi barazanar shure duk wani tayin da aka gabatar mata, dangane da batun makamashin nukiliyanta da ake ƙorafi a kansa, idan Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartad da ƙudurin sanya mata takunkumi, a taron da kwamitin sulhu na Majalisar zai yi yau a birnin New York. Wannan dai ita ce farkon amsar da Iran ɗin ta bayar a hukumance, ga kundin wani ƙudurin da ke bukatarta da ta dakatad da shirye-shiryen inganta sinadarin yureniyum kafin ƙarshen watan Agusta, ko kuwa ta huskanci takunkumin ƙasa da ƙasa da za a sanya mata. Tun ran juma’ar da ta wuce ne dai aka rarraba shirin ƙudurin ga mambobi 15 na kwamitin sulhun.