1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi barazanar mai da martani idan Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya mata takunkumi.

October 9, 2006
https://p.dw.com/p/BugV

Shugaba Mahmoud Ahmadinijad na ƙasar Iran ya lashi takobin ɗaukar fansa kan ƙasashen da za su amince da sanya wa ƙasarsa takunkumi a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda shirin makamashin nukiliyanta. Kafofin yaɗa labaran ƙasar dai ba su bayyana irin matakan da shugaban ke niyyar ɗauka ba. Sai dai Iran, wadda ita ce a jeri na biyu na ƙasashen da suka fi haƙo man fetur a ƙungiyar OPEC, ta ce ba za ta yi amfani da albarkatun manta wajen mai da martani ba: Wakilan ƙasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun da kuma Jamus, sun yarje kan tattauna batun sanya wa Iran ɗin takunkumi ne, bayan da ta ƙi miƙa wuya ga bukatunsu na ta dakatad da shirye-shiryenta na sarrafa sinadarin Yureniyum.