1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi barazanar sake kera makamashin nukiliya

Ramatu Garba Baba
April 22, 2018

Kasar Iran ta yi gargadin sake farfado da shirin kera makamashin nukiliya bayan da Amirka ta yi barazanar sauya mataki a yarjejeniyar da suka rattaba wa hannu kan dakatar da shirin a shekara 2015.

https://p.dw.com/p/2wSg4
Iran Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Ministan harkokin wajen kasar Javad Zariff ne ya sanar da hakan inda ya ce da zarar Amirka ta karya dokokin yarjejeniyar, Iran ba za ta jinkirta daukar matakin mayar da martani ba. An cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran bayan da aka shafe tsawon lokaci ana tattaunawa a tsakanin manyan kasashen duniya shida, a karkashin yarjejeniya, kasar ta Iran ta amince ta rage karfin yadda ta ke sarrafa sinadarin uranium inda aka yi alkawarin janye takunkumin da majalisar dinkin duniya ta garkama ma ta.

An kulla yarjejeniyar a lokacin gwamnatin Barack Obama, sai dai shugaba Donald Trump ya sha yin barazanar fitar da kasar daga shirin, sauran kasashen da aka cimma matsaya tare sun hada da Britaniya da Faransa da Rasha da Chana da kuma Jamus sai  Amirkan, wadannan kasashen na ci gaba da lallamin Trump kan mutunta wannan yarjejeniyar.