1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi tayin shawarwari ga komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia

August 27, 2006
https://p.dw.com/p/BulS

Ƙasar Iran, ta yi kunnen uwar shegu ,da buƙatar komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia , na ta yi watsi, da shirin ƙera makaman nuklea, kamin 31 ga watan da mu ke ciki.

Saidai, kakakin opishin ministan harakokin waje, ya jaddada kira, ga ƙasashe masu hannu da shuni, da ke shiga tsakanin wannan rikici, zuwa sabin shawarwari.

Hamid Reza Assefi, ya ce Iran shire ta ke, ta ci gaba da tantanawa domin samo bakin zaren warware wannan baddaƙƙala.

Saidai jim kaɗan kamin wannan jawabi, ƙasar Iran ta harba wani makami mai lizzami a matsayin gwaji.

Hukumomin tsaro na kasa, sunce wannan makami mai dogon zango ya cimma mizanin da su ke bukata.

A nasa gefe, ranar assabar mai zuwa, Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan, zai zuwa birnin Teheran, domin tantanawa da da hukumomin Iran, a game da rikicin makaman nuklea.