1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da sabon tayin Kungiyar EU game da shirin ta na nukiliya

May 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buxw

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad yayi watsi da sabon tayin da KTT ta yi, wanda ya bukaci Iran din ta daina aikace-aikacenta na sarrafa sinadarin uranium sannan a saka mata da wani jerin taimako. A wani jawabin da yayi a garin Arak dake tsakiyar Iran, shugaba Ahmedi Nijad ya ce kasarsa ba ta bukatar wannan taimako daga EU. Shugaban ya kara da cewa Iran ta taba tabka kuskure na dakatar da shirinta na nukiliya. Kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Jamus sun yi tayin taimakawa Iran da wata tashar samar da makamashin nukiliya mai amfani da ruwa idan gwamnatin Teheran ta yi watsi da shirin ta na nukiliya. A kuma halin da ake ciki an jinkirta wani taron manyan kasashen duniya da aka shirya yi ranar juma´a a birnin London don sake duba tayin da EU ta yiwa Iran.