1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da zargin da Amirak ta yi mata na rura wutar rikicin Iraki

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Busi
Iran ta musanta zargin da wani babban hafsan sojin Amirka yayi cewa ita ce babbar kasar da ke taimakawa masu ta da kayar baya a Iraqi. Kamfanin dillancin labarun Iran IRNA, ya jiyo kakakin ma´aikatar harkokin waje a birnin Teheran, Hamid Reza Asefi na cewa Iran ta yi watsi da zargin da wasu jami´an Amirka ke yi game da hannunta a rikicin Iraqi. Ya ce zargin na daga cikin kokarin da jami´an Amirka ke yi na rufe gazawarsu da rashin amincewa da kayen da suka sha a Iraqi. Kakakin ya kara da cewa kasancewar Amirka a yankin ta sabawa bukatun al´umar yankin da ma na Amirkawa. A ranar alhamis da ta gabata babban kwamandan Amirka a Iraqi Janar George Casey ya ce Iran ce babbar mai marawa tashe tashen hankula a Iraqi baya, kana kuma ya zargi gwamnatin Teheran da horaswa tare da ba da makamai ga kungiyoyin ´yan shi´a dake ta da kayar baya a Iraqi.