1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tace ba ja da baya a shirinta na nukiliya

January 13, 2006
https://p.dw.com/p/BvCS

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmedinejad yace ,shifa ba gudu ba ja da baya,akan shirin nukiliya na Iran,musamman a kokarin kasarsa na samarda makamashi,yace,turawa sun nemi Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya suna masu mana alkawari zasu bamu mai da zamuyi anfani da shi ,amma yace ta yaya zamu yarda da su ganin cewa sun kasa bamu koda magunguna ne.

Kasar Amurka da manyan kasashe 3 na Kungiyar Taraiyar Turai,a jiya sun kira taro na gaugawa na hukumar kare yaduwar nukiliya domin duba yiwuwar mika Iran gaban komitin sulhun domin ladabtar da ita,sai dai kasar Faransa a yau ta baiyana cewa lokaci bai yi ba da zaa yi batun lakabawa kasar Iran takunkumi,hakazalika kasar Rasha wadda take goyon bayan Iran ta bukaci Iran din da ta bada hadin kanta ga hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa.

A yanzu haka kasashen Rasha da Sin wadanda suka nuna rashin goyon bayansu ga batun lakabawa Iran takunkumi,sun shirya ganawa a mako mai zuwa domin tattauna wannan batu.

Kodayake jamian diplomasiya suna ganin cewa mai yiwuwa ne yanzu su amince da takunkumin ganin cewa Iran tayi kunnen uwar shegu da kiraye kiraye da suke yi mata na kada ta ci gaba da sarrafa sinadarin uraniyum.