1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Za a kare ofisoshin jakadanci

Ahmed SalisuJanuary 3, 2016

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce gwamnatinsa hukunta dun wanda ta samu da hannu a kone ofishin jakadancin Saudiyya da ke kasar da aka yi.

https://p.dw.com/p/1HXNs
Iran Teheran Rede Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne dazu bayan da wasu masu zanga-zanga suka afkawa ofishin jakadancin Saudi Arabiya da ke Tehran tare da cinna masa wuta a wani mataki na nuna fushinsu kan kisan da Saudiyya din ta yi wa malamin Shi'ar nan Nimr al-Nimr a ranar Asabar.

A wasu sakonni da ya aike da su ta shafinsa na Twitter, Rouhani ya ce wannan danye aikin da aka yi na kone ofishin jakadancin Saudiyya din aiki ne na wasu mutane da ya ce sun wuce gona da iri, a hannu guda ya ce gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen kare ofisoshin jakadancin kasashen duniya da ke kasar.

To sai dai a share guda ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na nuna rashin amincewarta da aiwatar da hukuncin kisa kan Nimr al-Nimr inda ya ce hakan ya saba wa dokokin addinin Islama sannan yin karen tsaye ne ga 'yancinsa a matsayinsa na dan Adam.