1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran za ta koma shawarwari da kungiyar EU a game da shirin nukiliya

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buw5

Iran ta ce tana fatan komawa teburin shawarwari da ƙungiyar tarayyar turai watakila ma kuma da washington. Ta ce to amma zata yi hakan ne kawai idan Amurkan ta nuna sanin ya kamata. Bugu da ƙari Tehran ta ce a shirye take ta shawarta yawan naurorin sarrafa sinadarin Uranium da zata yi amfani da su wajen binciken kimiya. To amma ta jaddada cewa ba zata dakatar da bunƙasa sinadarin Uranium ba kamar yadda kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya buƙata. Iran ta ce tana amfani da makamashin ne kawai domin samar da hasken wutar lantarki ga alumar ta. A ranar alhamis mai zuwa ne ƙasashe biyar masu wakilcin kujerar dundundun a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniyar za su gudanar da taro a birnin Vienna domin kammala shawarwari a game da moriyar da za su baiwa domin ta dakatar da shirin makamashin nukiliyar. A waje guda kuma Amurka ta baiyana farin ciki da jawabin kasar Iran na komawa shawarwari da kungiyar tarayyar turai kan batun nukiliyar. Kakakin fadar White House Tony Snow ya shaidawa yan jarida cewa gwamnatin Amurka ta yi maraba da shawarar kuma tana fata a wannan karon zaá cimma nasara.