1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran zata janye ajiyarta daga bankunan yammacin duniya

January 21, 2006
https://p.dw.com/p/BvBO

Iran ta ba da sanarwar cewa zata janye ajiyar kudaden musayarta na ketare daga bankunan kasashen yamma don kare su daga takunkuman MDD. Ko da yake manyan jami´an Iran ba su fadi inda zasu mayar da wadannan kudade ba, amma majiyoyin bankuna a Frankfurt sun ce gwamnatin birnin Teheran na shirin janye dala miliyan dubu 8 daga bankunan kasashen yamma ciki har da dala miliyan dubu 6 daga bankunan Turai. Wasu manazarta harkokin yau da kullum sun ce bisa ga alamu za´a mayar da kudaden ne a bankunan yankin GTT da kuma na kasashen Asiya. Amirka ta bayyana wannan mataki da cewa wani aiki ne na kebe kai. Gwamnatin birnin Washington dai na neman hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta yi karar Iran a gaban wkamitin sulhu akan shirinta na nukiliya.