1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IRAQ A YAU LITININ

August 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvha

Rahotanni daga kasar iraqi sun tabbatar da cewa,yan tawayen kasar sun halaka wannan dan kasar turkiyyan da sukayi garkuwa dashi,kamar dai yadda rahoton ya fito daga bakin wani babban jamii a ofishin jakadancin turkiyyan dake birnin bagadaza.

A wata sabuwa kuma,a jiya ne aka samu tashin wani bomb a wani churchi dake birnin na bagadaza.Wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma tare kuma da raunana wasu mutane hamsin.

Har ya zuwa yanzu dai baa gano wanda ya haddasa wannan tashin bomb ba,sai dai mahukuntan kasar ta iraqi,da kuma kasar amurka suna zargin shugaban yan tawayen nan kuma dan kungiyar alqaeda Abu Musab Alzarqawi,da kai wannan hari.

To a yau ne kuma mahukuntan na iraqi,suka yi kira ga alummar kasar,da cewa lokaci yayi da duk yan kasar zasu fara taka rawarsu wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar tare kuma da hadin kai.

Wannan hari dai a churchi ya kasance na farko da aka kai wa wani wurin bauta a kasar ta iraqi,hakan ne kuma ya sa chiristocin kasar suka taallaka wannan alamari da sojin kasashen ketare dake cikin kasar.

A cewar wata chirista Marie Butros,yar shekara talatin da biyar kuma maikaciyar asibiti.lafiya ake zaune tsakanin addinai a iraqi,sai wannan lokaci da wasu kasashen ke musu katsalandan a harkokin kasar su.

A hannu guda kuma,shugabannin shiawa a kasar irin su Muqtadr Sadr da kuma Ayatulla Ali Alsustani,sun yi kakkausan suka ga wannan hari,tare kuma da kira ga yan kasar dasu tashi tsaye wajen kare junan su,daga miyagu masu neman tarwatsa su.

Gashi dai chirista a kasar ta iraqi sun kai dubu dari takwas wanda ya kama dai dai da kashi uku daga cikin dari na kasar baki daya.amma kuma hakan bata taba faruwa ba sai a wannan lokaci.

Kamar dai yadda rahotanni a watan daya gabata suka bayyana yan tawayen kasar iraqin sun yi garkuwa da wasu yan kasashen kenya uku da yan india uku da kuma dan kasar masar daya,to har ya zuwa yanzu dai mahukuntan wadannan kasashe suna nan suna neman daidaitawa da yan tawayen domin su saki wadannan mutane.

Shi kuwa wannan dan kasar somaliyan da aka yi garkuwa dashi,tare da neman kamfanin daya ke yiwa aiki a iraqi su dakatar da aikin nasu,a yanzu haka kamfanin mallakar kasar kuwait sun amince zasu tsaida aikin nasu a iraqin,wanda kuma idan har sun yi hakan yan tawayen zasu saki wannan mutum.

Watanni hudu kenan yan tawaye a kasar iraqi,na garkuwa da mutane yan kasashe daban daban kusan ashirin da hudu a duniya,wanda wasu daga cikin irin wadannan mutane sun rasa rayukan su wasu kuma an sake su da ransu.

Maryam L.Dalhatu