1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ireland ta gabatar da shirin tsuke bakin Aljihu

November 25, 2010

Shirin na da nufin rage giɓin kasafin kuɗin ƙasar da kimanin euro biliyan 15 nan da shekaru huɗu

https://p.dw.com/p/QHeg
Priministan Ireland Brian CowenHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Ireland ta gabatar da tsauraran matakan tsuke bakin aljihu, waɗanda za su taimaka wajen ceto ƙasar  daga matsalolin basussuka da take fama dasu. Banda rage kashe-kashen gwamnati da kara haraji, matakan sun kuma haɗar da rage kuɗaɗen albashi, kazalika dubban mutane za su rasa ayyukansu. Wannan shiri da zai gudana har tsawon shekaru huɗu dai, na da nufin samarwa da gwamnati kimanin euro biliyan 15. Ana saran tattaunawar tsakanin Ireland  da ƙungiyar Tarayyar Turai dangane da ceto, zai bawa ƙasar tallafin euro biliyan 85. Priministan Ireland Brian Cowen, wanda gwamnatinsa ke dab da rushewa, ya yi ikirarin cewar wannan shiri nasa zai sake farfaɗo da ƙasar daga matsalolin tattalin arziki. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce a shirye Jamus take wajen taimakawa Ireland, sai dai ya zamanto wajibi ƙungiyar EU ta ɗauki matakan takaita hada-hadan kasuwanni tare da tabbatar da cewar masana'antu masu zaman kasansu sun rataya alhakin wasu daga cikin irin waɗannan matsaloli na bashi da ƙasashe ke faɗawa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Umaru Aliyi