1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta kai hari ga ma'aikatun mai a Libiya

Salissou BoukariFebruary 22, 2016

Wasu mutane da ake zaton 'yan kungiyar IS ne sun kai hari a karshen makon da ya gabata ga wuraran fitar da man fetir ta Fida da ke kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/1HzxX
Erdöl im Iran

Wannan labari ya fito ne a ranar Litinin (22.02.2016) daga Moustafa Sanalla da ke a matsayin shugaban ma'aikatar man fetir ta kasar ta Libiya ta NOC (National Oil Corporation). Ma'aikatar man ta Fida dai na a Kudu maso yammacin wasu ma'aikatun na man da suka hada da na Sider da kuma na Ras Lanouf da su ma suka fuskanci hare-haren ta'addanci daga 'yan kungiyar ta IS tun a watan Janairu da ya gabata.

Kasar ta Libiya dai ta yi zaman fitar da danyan man da ya kai ganga dubu 360 zuwa dubu 370 a ko wace rana kafin tashin hankalin da ya kifar da gwamnatin marigayi Shugaba Mohamar Kadhafi a shekara ta 2011.