1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isar’ila ta ce a shirye take ta tattauna batun musayar fursunoni.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bukz

Isra’ila ta bayyana shirinta na shiga shawarwarin musayar fursunoni tsakaninta da Lebanon, inda ta ce za ta sako fursunonin Lebanon da ke hannunta, idan ƙungiyar Hizbullahi ta miƙa wa gwamnatin Lebanon sojojinta guda biyu da take garkuwa da su. Da yake bayyana haka yau a birnin ƙudus, wani babban jami’in gwamnatin Isra’ilan ya ce ƙasarsa ba za ta da amince da tattaunawa da ƙungiyar Hizbullahi ba, ko da ta kan mai shiga tsakani ne. Gwamnatin birnin ƙudus za ta yi shawarwari ne kawai da gwamnatin Lebanon, inji jami’in. Ya ƙara da cewa, tuni an bayyana wa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan matsayin Isra’ilan, yayin ziyararsa a birnin Ƙudus jiya laraba.

Mashrahanta dai na ganin wannan sanarwar da Isra’ilan ta bayar kamar nuna sasssauci ne ga matsayin da ta ɗauka a da, na cewa ta neman sako sojojin nata ne ba da wani sharaɗi ba.