1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isar’ila ta ce za ta kai jami’an Hukumar Falasɗinawan da ta cafke gaban shari’a.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burj

Rikicin da ake yi yanzu tsakanin Isara’ila da Hukumar Falasɗinawa sai ƙara tsananta yake yi. Mataimakin Firamiyan Isra’ila, Shimon Peres, ya ce ƙasarsa za ta hukuntad da duk jami’an Hukumar Falasɗinawan da ta cafke. A cikin wata fira da ya yi da gidan talabijin Amirkan nan CNN, Shimon Peres ya ce ƙararrakin da za a ɗauka game da jami’an sun haɗa ne da goyon baya, da kuma samun hannu a ayyukan ta’addancin da aka gudanar kan gwamnatin farar hular Isra’ila.

A makon da ya gabata ne dai Isra’ilan ta kai hari kan ginin ma’aikatar harkokin cikin gida ta Hukumar Falasɗinawan da ke Gaɓar Yamma, sa’annan kuma ta kame ’yan kungiyar Hamas da dama, a cikinsu har da ministoci 8 da kuma ’yan majalisa fiye da 20. Ta kuma soke izinin zaman wasu ’yan majalisar guda 4 a birnin ƙudus.

A yau lahadi ma, sai da jiragen saman yaƙin Isra’ilan suka kai hare-haren kan kafofin Falasɗinawan, inda suka jefa bam kan ofishin Firamiyan Falasɗinawan Isma’il Haniye. Ƙasar bani Yahudun dai ta yi barazanar yin amfani da duk ƙarfin sojinta wajen ceto ɗaya daga cikin dakarunta da wani rukunin ’yan ƙungiyar Hamas ɗin ya yi garkuwa da shi.