1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isma´il Haniya yayi kira da a kafa gwamnatin hadin kan Falasdinu

January 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuUa
FM Falasdinawa Isma´il Haniya ya yi kira da a kafa wata gwamnatin hadin kan kasa. A cikin wani jawabi da yayi ta gidan telebijin Haniya yayi kira da a kawo karshen tashe tashen hankula tsakanin kungiyarsa ta Hamas da kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Da farko jami´an kungiyoyin biyu da ba sa ga maciji da juna sun ce ana samun ci-gaba a tattaunawar da bangarorin biyu ke yi a boye da nufin kulla wani kawance. Rahotanni sun yi nuni da cewa kimanin makonni biyu da suka wuce aka fara tattaunawar tsakanin shugaban Hamas Khaled Meshaal da wakilan kungiyar Fatah ta Mahmud Abbas. Akalla Falasdinawa 30 aka kashe sakamakon arangama da magoya bayan sassan biyu ke tun bayan da shugaba Abbas ya yi kira da a gudanar da zabe na gaba da wa´adi a wani yunkuri na kawo karshen dambaruwar siyasa cikin hukumar ta Falasdinu.