1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela na ci gaba da kai hare hare a Lebanon

August 2, 2006
https://p.dw.com/p/BuoA

Dakarun sojin Israela na ci gaba da kaddamar da hare hare mafi muni ga dakarun kungiyyar Hizbullah. Hari na baya bayan nan shine wanda ya haifar da yin awon gaba da wasu mambobi na kungiyyar ta Hizbulla izuwa Israela.

An cafke wadannan mambobi ne a wani harin mamaye da sojin na Israela suka kai, izuwa wani asibiti dake mallakar kungiyyar ta Hizbullah dake garin Baalbek.

A cewar rahotanni, ire iren wadannan hare hare ya kuma haifar da kisan wasu sojin Lebanon guda uku.

Bayanai dai sun shaidar da cewa dakarun sojin na Israela sun kai hari ne kann cibiyar sojin kasar, bisa hasashen cewa dakarun Hizbullah nada ofisohi a yankin.

Ya zuwa yanzu dai an kiyasta cewa mutane kusan 7 ne suka rasa rayukan su wasu kuma da dama suka jikkata, a sakamakon sabbin hare haren.

A kuwa yayin da ake da kiraye kirayen kawo karshen wannan balahira, a daya hannun kuma kafafen yada labaru sun rawaito mataimakin faraministan kasar, wato Shimon Perez na fadin cewa nan gaba za a iya daukar makonni kafin Israela ta kawar da duk wata barazana da kungiyyar ta Hizbullah zata iya kawo mata.