1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela ta kai sabbin hare-hare a Gaza

Ibrahim SaniJanuary 3, 2008
https://p.dw.com/p/CjqZ

Dakarun sojin Israela sun halaka tsagerun Falasɗinawa uku a zirin Gaza. Hakan ya biyo bayan sumamen da sojin ke ci gaba da kaiwa ne izuwa yankin. Matakin a cewar Israela nada nasaba ne da dakile fitinar tsagerun, dake ci gaba da kai musu hare-haren rokoki. Ci gaba da rikice-rikice a yankin, abune a cewar rahotanni daka iya kawo tsaiko game da tattaunawar sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu. A mako mai zuwa ne shugaba Bush zai ziyarci yankin, don assasa batu na zaman lafiya a tsakanin Israelan da yankin Falasɗinawa. Ana sa ran Mr Bush zai gana da Mr Olmert da Abbas a lokacin wannan ziyara