1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela ta kai sabbin hare hare a zirin Gaza

December 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvEs

Jiragen Israela masu saukar ungulu sun kai wasu hare haren rokoki a arewacin zirin Gaza da jijjibin safiyar yau talata.

Wani bapalasdine daya ganewa idon sa ya shaidar da cewa daya daga cikin rokokin ta sauka ne a cikin wani gini mallakar jamiyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas,daya rokar kuwa ta sauka ne a wani guri na daban sabanin inda aka nufi data lalata.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton rasa rai ko kuma jikkata,sakamakon wadannan rokoki da aka harbo izuwa zirin na gaza.