1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela zata janye kawanyar da tayiwa Libanon

September 6, 2006
https://p.dw.com/p/Buka

Kasar Israela tace nan bada dadewa ba, zata janye kawanyar ruwa data sama da tayiwa kasar Libanon.

A cewar kasar ta Israela, zata yi hakan ne sannu a hankali don bawa dakarun sojin Mdd damar karbar ragamar jagorancin harkokin tsaro a yankin, a wani mataki na hana dakarun kungiyyar Hizboullah tasiri a yankin.

A dai jiya talata ne kafafen yada labaru suka rawaito sakataren Mdd, Mr Kofi Anan na jaddada fatan sa na cewa, nan da yan kwanaki kadan masu zuwa Israela zata janye kawanyar da tayiwa kasar ta Libanon.

Aiwatar da wannan mataki dai yadda aka tsara abu ne da zai share fagen zuwan dakarun sojin Jamus cikin tawagar dakarun Mdd izuwa kasar ta Libanon.

Ya zuwa yanzu dai tuni mahukuntan Libanon suka amince da zuwan dakarun sojin na Jamus, to amma zata yi hakan a hukumance ne idan Kasar ta Israela ta kammala janye kawanyar da tayiwa kasar.