1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila da Pakistan sun tattauna karo na farko

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 2, 2005

Ministocin harkokin wajen Israila da Pakistan sun gana a Istanbul,karo na farko dama su suka suka ganin wani mataki ne na kulla dangantaka

https://p.dw.com/p/BvZy
Silvan Shalom da Khursheed Mahmood
Silvan Shalom da Khursheed MahmoodHoto: AP

Ministan harkokin wajen Pakistan Khurshid Mahmood Kasuri bayan tattaunawar tsakaninsa da takwararsa na Israila Silvan shalom,yace kasar Pakistan ta yanke shawarar kulla yarjejeniya da Israila bayan shekaru da tayi tana daya daga cikin kasashe da suke sukar kasar Israilan.

A nashi bangare kuma Minisatan harkokin wajen Israila Silvan Shalom,cewa yayi Israila tana fatar cewa wannan taron zai kai ga kafa huldar diplomasiya tsakanin Israila da Pakistan kamar yadda suke fatar kullawa da sauran kasashen larabawa.

Sai dai kuma shugaban kasar Pakistan Parvez Musharraf yace Pakistan ba zata amince da kasancewar Israila kasa ba har sai an kafa yantacciyar kasar Palasdinu.

A halin yanzu dai kasar Israila tana da huldar diplomasiya tsakaninta da kasashen musulmi guda hudu,wato,Masar,Jordan,Turkiya,da Mauritania,tana kuma da matsakaicin huldar kasuwanci tsakaninta da kasashen Maroko,Tunisia da Qatar.

Wannan tattaunawar tsakanin Israila da Pakistan tazo ne kafin wani jawabi da shugaban Parvez Musharraf zai yiwa ga shugabannin yahudawa wajen wani taron addinai wanda majalisar yahudawa ta duniya ta shirya a birnin New york cikin wannan wata da muke ciki.

Masu lura da alamurra sunyi imanin cewa,Pakistan tana wani yunkuri ne na sassauta dangantakun tsaro dana soji tsakanin Israila da India,wadanda suka kulla kawance a shekarar 1992.

Babbar jamiyar musulmi ta Pakistan tayi Allah wadai da kokarin Pakistan na maida kawance da Israila,jamiyar tace zata kakkafa bakaken tutoci a koina cikin kasar domin nuna bakin cikinta game da wannan tattaunawar.

Hakazalika kungiyar HAMAS,da ta lashi takobin kawo karshen Israila,ta bukaci kasar Pakistan data sake duba wannan yunkuri nata da idon basira.

Kasar ta Pakistan tun farko tana cikin jerin kasashe dake goyon bayan kawo karshen mamayar da Israila tayiwa yankunan Palsdinu tun a lokacin yakin yankin gabas ta tsakiya a 1967.

A shekara 2001 ne dai,a lokacinda aka zabi Sharon a matsayin Prime Minista, shugaba Musharraf ya taba cewa, sabon Prime Ministan Israilan shine kadai zai iya daukar matakan kawo zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

A wani labarin kuma wasu yan majalisa sun fice daga taron majalisar dokokin Pakistan yayinda magoya bayansu suke shirya gangami bayan sallar jumaa yau domin yin Allah wadai da tattaunawa tasakanin Israila da Pakistan,wanda wasu masu suka suke cewa wani mataki ne na neman amincewa da kasar Israila a matasayin kasa.

Ameer ul-Azeem,kakakin gamaiyar jamiyun musulmi guda shida ya da ya baiyana haka,ya kuma zargi shugaba Parvez Musharraf da shirya tattaunawar ba tare da tuntubar yan majalisa ba tare kuma da laifin shirya aikawa da tawagar kasar Pakistan zuwa birnin Kudus.

A bayan sallar jumaar yau yan kungiyar Islamis Jihad suka yi maci daga Beit Lahiya zuwa Jabaliya suna masu kona tutocin Israila da na Amurka domin nuna adawa da tattaunawa tsakanin Israila da Pakistan