1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila na ci-gaba da kai farmakin gama gari a Zirin Gaza

November 3, 2006
https://p.dw.com/p/BudS

Wasu sabbin hare hare da Isra´ila ta kai a arewacin Zirin Gaza da sanyin safiyar yau juma´a ta halaka akalla sojojin sa kai na Falasdinawa su 8. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce mutum 4 dukkan ´ya´yan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun mutu a wani harin roka da Isra´ila ta kai kan motarsu a birnin Gaza. Da farko kuwa wasu Falasdinawa 4 sun rasa rayukansu a wasu hare hare guda biyu da jiragen saman yakin Isra´ila ta kai a kusa da sansanin ´yan gudun hijira na Jabaliya. Har yanzu kuwa sojojin Isra´ila na gwabza kazamin fada da sojojin sa kai na Falasdinawa a garin Beit Hanun. A wani labarin kuma sojojin Bani Yahudu sun yiwa wasu ´yan bindigan Falasdinawa kawanya a wani masallaci dake tsakiyar garin. A dai halin da ake ciki motocin rusa gine gine sun buge wani sashe na masallacin don tilastawa Falasdinawa da suka nemi mafaka a ciki su mika kai. Kawo yanzu Falasdinawa 20 aka kashe tun bayan da Isra´ila ta fara kai sabon farmaki a ciki da wajen garin Beit Hanun a ranar laraba da ta gabata.