1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a ƙasar Lebanon.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupU

A rana ta 12 a jere, tun da ta fara kai farmaki a ƙasar Lebanon, Isra’ila na ci gaba da yi wa yankunan Beirut da sauran yankunan gabashi da kudanci ƙasar hadarin bamabamai. Ban da kame ƙauyen Maroun al-Ras a kudancin Lebanon da ta yi jiya, Isra’ilan ta kuma yi wa garin Sidon luguden wuta, duk da cewa a nan ne mafi yawan fararen hular da suka ƙaurace wa matsugunansu a kudancin Lebanon, suka nemi mafaka. Har ila yau dai rahotanni sun ce Isra’ilan na ta ƙara girke dakarunta a kann iyakarta da Lebanon, abin da ke alamta cewa tana da niyyar afka wa ƙasar da sojojin igwa. Kawo yanzu dai alƙaluma sun ce fiye da mutane ɗari 3 da 70 ne suka rasa rayukansu a ƙasar Lebanon, mafi yawansu kuma, fararen hula, tun da Isra’ilan ta fara kai hare-harenta a ƙasar.