1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burv

Jiargen saman yaƙin Isra’ila sun kai wani sabon hari a birnin Gaza, inda suka jefa bam kan ofishin Firamiyan Falasɗinawa Ismail Haniya. Rahotanni sun ce Firamiyan ba ya cikin ginin a lokacin da aka jefa bam ɗin, sai dai harin y ata da gobara, sa’annan kuma, masu kare lafiyar Firamiyan su uku sun rasa rayukansu. Isra’ilan dai ta iza wuta a hare-harenta a zirin Gazan ne don angaza wa ’yan ta kifen Falasɗinawan su sako wani sojanta da suka kame a makon da ya gabata.

Bayan harin, Isma’il Haniya, ya ziyarci gun don ya gano wa idanunsa irin ɓarnar da dakarun Isra’ilan suka haddasa. A nan ne kuma ya yi Allah wadai da abin da ya kira „manufar rashin hankali“ da ƙasar bani Yahhudun ta sanya a gaba. Ya kuma dai yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta angaza wa Isra’ilan don ta tsai da samamen da take yi wa zirin na Gaza.

A halin da ake ciki dai, shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin da ake yi wajen cim ma sako sojan Isra’ilan, duk da wasu rahotannin da ke nuna cewa an sami cijewar shawarwarin. Tuni dai Isra’ila ta yi watsi da bukatun Falasɗinawan, na ta sako fursunoninsu dubu da take tsare da su a gidajen yarinta, kafin su ma su sako sojanta da suka yi garkuwa da shi.