1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila na ci gaba da kai hare hare a zirinn Gaza

July 6, 2006
https://p.dw.com/p/BurU

Ƙasar Israela na ci gaba da mamaye sassa daban-daban na zirin Gaza a yunƙurin ta, na gano Gilad Shalit, wani soja, da Palestinawa su yi garkuwa da shi tun ranar 25 ga watan juni.

Daga daren jiya, zuwa sahiyar yau, rundunar Israela ta kai hari, da ya hadasa mutuwar mutum 1.

Praminsita Ehud Olmert, ya ce hare hare kam, sai abunda ya ci gaba, muddun Palestinawa ba su yi belin Shalit ba.

A sauran sassa na zirin Gaza, jami´an tsaron Isra´ila na ci gaba da sintiri.

A nasu gefen, dakarun Hamas na maida martani, ta hanyar harba rokoki, a wasu wurare mallakar Isra´ila.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condolesa Rice, ta yi kira ga yan Hamas, da su yi belin sojan da su ka kama, a yayin da su ka nace, kan cewar, sai Isra´ial ta yi hurhuren sa, da dubunan pirsinoni Palestinawa, da ta ke tsare da su.

Shima Sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan, ya gayyaci bangarorin2, da su nuna dattako da sannin ta kamata.

Shugaban ƙungiyar Hamas Khaled Michel, da ke gudun hjira a birnin Damascus, na ƙasar Syria, ya ce a shire ya ke, ya hau tebrin shawara, don gano bakin zaren warware rikicin amma, da sharaɗin Isra´ila, ta alkawarta yin belin Pirsinonin Palestinu.