1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila na cigaba da luguden wuta a Gaza

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurN

Sojojin Israila sun ƙara tsaurara farmaki a yankin zirin Gaza inda suka kashe a ƙalla Palasɗinawa ashirin a luguden wuta da suka yi da jiragen sama. Israilan ta ce wani sojin ta ɗaya ya rasa ran sa yayin wata arangama a arewacin Gaza. Wannan dai shi ne farmaki mafi muni tun bayan da P/M Israila Ehud Olmert ya bayar da umarnin tura sojoji da tankunan yaƙi zuwa cikin Gaza. P/M Palasɗinawa Ismaila Haniya, ya yi kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa su tsoma baki domin dakatar da Israila daga cigaba da kai farmaki a Gaza, yana mai baiyana luguden wutar da cewa cin zali ne da keta mutuncin alúmar Palasɗinawa. A makon da ya gabata ne dai Israila ta ƙaddamar da kutse a yankin Gaza bayan garkuwa da sojin ta guda da mayakan sa kai na Hamas suka yi. A waje guda kuma kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya fara tattaunawa wani daftarin ƙudiri da ƙasashen larabawa suka gabatar wanda ya buƙaci Israila ta dakatar da farmakin ta kuma gaggauta janyewa daga yankin na Gaza, sai dai Amurka da Faransa sun baiyana daftarin da cewa ya karkata ga bangare guda. Daftarin ƙudirin ya yi kira ga rukunin nan hudu waɗanda ke shiga tsakani domin samar da wanzuwar zaman lafiya a gabas ta tsakiya da suka haɗa da ƙungiyar tarayyar turai da Rasha da Amurka da kuma majalisar ɗinkin duniya su ɗauki matakan gaggawa da suka haɗa da ƙarfafa yarda da aminci a tsakanin bangarorin domin komawa ga shirin tattauna zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.